Hukumar Raya Arewa maso Yamma na shirin samar da jarin dala miliyan 200 a harkar noma

Hukumar Raya Arewa maso Yamma na shirin samar da jarin dala miliyan 200 a harkar noma

Hukumar Cigaban Arewa maso Yamma (NWDC) na shirin kulla wata babbar yarjejeniya ta zuba jari a fannin noma da darajarsa ya kai dala miliyan 200 tare da abokan hulɗarta na ƙasashen waje.

Wannan shirin dai ya haɗa da kamfanin Shanghai Integrated Infrastructure Development Limited (SIIDL) da kuma Peerless Advisory Limited, waɗanda wakilansu suka kai ziyarar aiki ga Hukumar a makon nan domin bayyana sha’awarsu.

Idan aka kammala yarjejeniyar, ana sa ran za a mayar da hankali kan manyan kayayyakin gona da suka haɗa da gero, shinkafa, alkama, zogale, dawa da kuma zobo, tare da samar da sabbin na’urorin noma na zamani da kuma horar da manoma.

Rahoton ya nuna cewa kamfanin SIIDL shi ne zai kasance babban mai saka jari inda zai samar da kashi 80 cikin 100 na kuÉ—in daga waje, yayin da NWDC za ta bada ta ta gudunmuwa ta fuskar fili da kuma taimakawa wajen samun izinin gwamnati.

Shugabancin Hukumar ya bayyana cewa wannan yunƙuri na daga cikin burinta na dogon lokaci na buɗe manyan damammakin noma a Arewa maso Yamma, tare da gina haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu da za ta haifar da amfani ga al’umma da kuma tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)