
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS, ta shigar da ƙarar jagororin ƙungiyar Ansaru biyu, bisa zarginsu da hannu a wasu hare-hare a Najeriya.
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS, ta shigar da ƙarar jagororin ƙungiyar Ansaru biyu, bisa zarginsu da hannu a wasu hare-hare a Najeriya.
Â
Makonni uku da suka gabata kenan bayan da hukumoin Najeriya suka sanar da kama mutanen biyu, waɗanda ake zargi da hannu a kitsa munanan hare-hare a faɗin ƙasar.
Â
Mutunen biyu su ne: Mahmud Usman, da aka fi sani da Abu Bara’a, da aka bayyana a matsayin Sarkin Ansaru, tare da mataimakinsa, Mahmud Al-Nigeri, wanda aka fi sani da Malam Mamuda.
Â
Hukumar ta DSS na tuhumarsu da laifukan da suka ƙunshi: ta'addanci da ɗaukar nauyin ayyukan ƙungiyar, da ɗaukar sabbin mambobi, tare da shirya munanan hare-hare a faɗin Najeriya.
Â
An dai zargi mutanen biyu da hannu a kitsa harin Gidan Yarin Kuje a watan Yulin 2022, inda fiye da fursunoni 600, ciki har da waɗanda ake zargi da kasancewa mayaƙan Boko Haram.