Jahar ondo

An kama jami’an rundunar tsaro ta Amotekun biyu bisa zargin satar koko a Ondo

An kama jami’an rundunar tsaro ta Amotekun biyu bisa zargin satar koko a Ondo

Jami’an rundunar tsaro ta jihar Ondo, wato Amotekun Corps,  su biyu sun shiga hannu bisa zargin satar koko a karamar hukumar Idanre ta jihar.

Wadanda ake zargin, da aka bayyana sunayensu da Ajayi Adebusuyi mai shekaru 45 da kuma Oluwadare Olubodun mai shekaru 42, an ce an cafke su a cikin gonar koko yayin aikin sintiri a kusa da sansanin Gbalegi a Idanre.

Rahotanni sun nuna cewa mai kula da gonar, Friday Abbah, ya sanya ido a gonar sakamakon yawaitar satar koko da ake fuskanta a wurin.

A yayin wannan sintirin ne aka ce an kama jami’an biyu dauke da kwakwan koko da ake kyautata zaton sun sata, wanda aka kwato a matsayin hujja.

Wani mazaunin garin, mai suna Abel, ya bayyana cewa an mika wadanda ake zargin nan take zuwa ofishin ‘yan sanda na  Idanre.

Da yake tabbatar da lamarin a ranar Juma’a, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, DSP Olayinka Ayanlade, ya ce an kama mutanen ne bayan korafe-korafen da masu gonaki suka shigar.

Ya ce yanzu haka suna hannun jami’an tsaro, kuma an mika batun zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha (SCID) domin ci gaba da bincike.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)