Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne,
Wasu 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a ranar Juma’a, sun kashe jami’an Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC) guda takwas da ke bakin aiki a kamfanin BUA Cement da ke Okpella, karamar hukumar Etsako East, jihar Edo.
Wani babban jami’in hukumar a jihar ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya ce an sace wani Bature dan kasar China, yayin da aka kubutar da wasu 'yan uwansa hudu daga hannun masu garkuwar.
Jami’in ya kuma ce mutane hudu sun jikkata a harin, kuma suna karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba. Ya kara da cewa za a fitar da sanarwa ta hukuma daga hedikwatar hukumar da ke Abuja.
A cewarsa:Â Â
> “Gaskiya ne, 'yan bindiga sun kashe mambobinmu guda takwas, amma za a fitar da cikakkiyar sanarwa daga Abuja daga baya yau