Manoman albasa a Jihar Jigawa sun yi asarar albasa da darajarta ta kai kusan naira biliyan É—aya sakamakon amfani da irin shuka marar inganci a lokacin daminar da ta gabata.

Manoman albasa a Jihar Jigawa sun yi asarar albasa da darajarta ta kai kusan naira biliyan É—aya sakamakon amfani da irin shuka marar inganci a lokacin daminar da ta gabata.

Shugaban Ƙungiyar Manoman Albasa ta Jihar, Malam Dauda Marma, ne ya bayyana hakan a zantawarsa da gidan Rediyon Jigawa.

Ya bayyana cewa wasu ’yan kasuwa marasa gaskiya sun rarraba wa manoma irin shuka daga ƙasar Morocco mara inganci, wanda hakan ya janyo musu tafka babbar hasara.

Ya ƙara da cewa irin albasa ɗin an shigar da shi cikin jihar daga jihohin Kebbi da Yobe.

Malam Dauda ya yi gargadin cewa daga yanzu duk wanda aka samu da laifin sayar da irin shuka marar inganci a Jigawa za a É—auki mataki a kansa.

Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar na ƙoƙarin ganin an kafa kasuwar albasa a garin Marma da ke Ƙaramar Hukumar Kirikasamma domin bunƙasa noman albasa, kasancewar kasashen Afirka na nuna sha’awar amfanin gonar Jigawa.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)