
Majalisar Dattawa ta hana Sanata Natasha komawa majalisa duk da cikar wa’adin dakatarwarta
Majalisar Dattawa ta hana Sanata Natasha komawa majalisa duk da cikar wa’adin dakatarwartaÂ
Majalisar Dattawa ta ce Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ba za ta iya komawa kujerarta ba duk da cikar wa’adin dakatarwarta na watanni shida.
Sanatan Kogi ta Tsakiya ta rubuta wa majalisar tana sanar da karewar dakatarwar da aka yi mata tun ranar 6 ga Maris, tare da nuna niyyarta ta koma aiki.
Sai dai a wasikar da Mukaddashin Magatakardar Majalisar, Yahaya Danzaria, ya aike mata, ya ce batun dakatarwar tana gaban kotu, kuma har sai an kammala shari’a sannan majalisar za ta dauki matsaya.
Nagarifmradio