
Jerin Wadanda Ba za su biya haraji ba a Najeriya
Jerin Wadanda Ba za su biya haraji ba a Najeriya: Duba idan kana ciki....
A wata hira da aka yi da Shugaban kwamitin gyaran haraji, Mr Taiwo Oyedele a tashar Channels ranar Talata, 8 ga watan Satumba, ya bayyana cewa sama da kashi 97 na yan Najeriya ba zasu biya haraji ba kwata-kwata, Mr Taiwo ya bayyana jerin Wadanda biyan sabon harajin ba zai shafe su ba kamar haka
1 Masu karban mafi karancin Albashi na 70k zuwa kasa
2 wadanda kudin shigarsu bai zarce dubu 100 ba a wata
3 'yan kasuwa masu jarin kasa da Naira Milyan 2
4 Kamfanoni da a da ake karban haraji a hannunsu duk da kadararsu bata haura milyan 25 ba, yanzu sai kadararsu ta kai Naira Milyan 100 sannan za su biya haraji
6 Wadanda ke biyan tarin haraje- haraje ma ba a barsu a baya ba, domin daga sabuwar shekarar 2026 za su fara biyan haraji daya tal , kuma mafi karanci
Ko ta yaya mutum zai gane cewa bai cancanci biyan haraji ba? Mr Oyedele ya ce tuni suka tanadi hatimi a manhajar QR kan shafin yanar gizo na tsarin harajin, inda duk mai bukatar sanin matsayinsa zai je ya dauki hoton hatimin QR din ya zura sunansa da bayanin kudaden shigarsa don sanin ya dace ya biya haraji ko a
Nagarifmradio