Ƙasar Qatar za ta karɓi bakuncin taron koli na gaggawa na kasashen Larabawa da Musulmi a ranar Lahadi, domin tattaunawa kan harin Isra’ila da ya girgiza yankin.

Ƙasar Qatar za ta karɓi bakuncin taron koli na gaggawa na kasashen Larabawa da Musulmi a ranar Lahadi, domin tattaunawa kan harin Isra’ila da ya girgiza yankin.

A wani martani, Qatar ta kira Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da “mara hangen nesa kuma sakarai” bayan tuhumar da yayi na cewa Doha tana ba da mafaka ga shugabannin Hamas.

Hare-haren Isra’ila sun yi sanadin mutuwar akalla mutane 16, yayin da sojojin Isra’ila suka bayyana cewa za su ƙara Kani wajen luguden wuta A birnin Gaza.

Duk da kiran ake yi  ga Isra'ila Akan ta bar barin Gaza, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce har yanzu tana nan tana gudanar da ayyukanta na kiwon lafiya.

Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa tun bayan fara yaƙin, akalla Palasɗinawa 64,656 suka rasa rayukansu, yayin da 163,503 suka jikkata a Gaza.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)