Gwamna Idris ya dakatar da Kwamishinan Lafiya

Gwamna Idris ya dakatar da Kwamishinan Lafiya

Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dokta Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya amince da dakatar da Kwamishinan Lafiya na Jihar, daga yau É—in nan.

Wannan matakin ya biyo bayan umarnin Gwamnan da ya bukaci Kwamishinan ya bayar da hujjoji masu ƙarfi da za su hana ɗaukar matakin ladabtarwa a kansa saboda sakaci da aiki da kuma rashin nuna kishin aikinsa a matsayin Kwamishina.

Da wannan umarni, an dakatar da Kwamishinan daga kujerarsa har zuwa wani lokaci.

Gwamna Idris ya sake jaddada aniyarsa ta tabbatar da ɗawainiya da gaskiya a cikin shugabanci, ladabtarwa da kuma ingantaccen isar da ayyuka a dukkan sassan gwamnati, inda ya ce dole ne duk wani jami’in gwamnati ya tabbatar da amincewar da aka nuna masa.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)