Malami ya kai ƙara ga NSA, Sufeto Janar, DSS da sauran shugabannin tsaro kan zargin shigo da 'yan daba da mayaƙan haya zuwa Kebbi

Malami ya kai ƙara ga NSA, Sufeto Janar, DSS da sauran shugabannin tsaro kan zargin shigo da 'yan daba da mayaƙan haya zuwa Kebbi

Abubakar Malami SAN, CON, tsohon Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na Tarayya, kana jagoran jam’iyyar *African Democratic Congress (ADC)* a Jihar Kebbi, ya kai ƙara zuwa ga Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Darakta Janar na Hukumar DSS, da kuma Kwanturola Janar na Hukumar Shige da Fice da ta Civil Defence, inda ya nuna damuwa kan yunkurin da ake zargin wasu ‘yan siyasa da shi na tayar da tarzoma a Jihar Kebbi ta hanyar shigo da 'yan daba, mayaƙan haya daga ƙasashen waje da kuma safarar makamai ta boye.

A cikin ƙarar da aka rubuta ranar 10 ga Satumba, 2025, Malami ya bayyana cewa akwai hujjoji masu ƙarfi da ke tabbatar da cewa ana haɗin guiwa da wasu mayaƙa daga ƙasar Nijar, kuma ana basu makamai ta hanyoyi ba bisa ka’ida ba. Ya ce an shirya amfani da su wajen kai hare-hare kan jama'a, tsoratar da ‘yan adawa da kuma karya zaman lafiya a jihar.


Malami ya ce wannan barazana ba zato-ba tsammani ba ce, domin yana da hujjojin sirri da kuma abin da ya faru da shi kai tsaye. Ya ambaci wani hari da aka kai masa da wasu ‘yan asalin jihar a ranar 1 ga Satumba, 2025, wanda ya ce an kai harin ne ba tare da tsoron jami’an tsaro ba.

Ƙarar ta kuma zargi Gwamnan Jihar Kebbi, Comrade Nasir Idris, da wasu abokan aikinsa da hannu a cikin wannan al’amari, tare da ambato dangantaka da ƙungiyar ta’addanci ta *Lakurawa*. Ya bayyana lamarin a matsayin “gaggawar matsalar tsaron ƙasa” da ta wuce siyasar jihar, tana barazana ga ikon ƙasar da zaman lafiyar cikin gida.

Malami ya roƙi NSA da sauran shugabannin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa ta hanyar haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro, kula da iyakokin ƙasa don hana shigo da mayaƙa da makamai, da kuma gudanar da bincike mai zurfi kan zargin haɗin gwiwa da ake yi wa jami’an gwamnati da ‘yan ta’adda.

An aika da kwafin ƙarar zuwa ga shugabannin DSS, ‘Yan Sanda, Shige da Fice da Civil Defence, domin nuna mahimmancin lamarin.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)