
Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin litar mai zuwa Naira 841
Matatar man Dangote ta sanar da rage farashin litar mai zuwa Naira 841, tare kuma da fara jigilar rarraba man fetur kyauta ga gidajen man Nijeriya daga ranar Litinin
Kamfanin Dangote zai fara rabon man fetur kyauta daga ranar Litinin, inji rahoton jaridar PUNCH.
Mai magana da yawun Kamfanin Dangote, Anthony Chiejina, ya shaidawa wakilinmu cikin wata sanarwa cewa za a fara wannan tsarin ne a yankin Kudu maso Yamma, Babban Birnin Tarayya Abuja, da jihohin Kwara, Delta, Rivers da Edo.
Ya kara da cewa matatar man ta Dangote ta rage farashin sayar da man fetur zuwa *N841 kowace lita a Legas da Kudu maso Yamma, da N851 a Abuja, Edo, Kwara, Rivers da Delta.
Ya ce: “Za mu fara rabon man fetur kyauta a ranar Litinin. Za mu fara da Legas da Kudu maso Yamma, Abuja, Kwara, Delta, Rivers da Edo. Rage farashin zai fara aiki ne daga ranar Litinin lokacin da rabon kyautar zai fara.”
Nagarifmradio