Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan noma kyauta ga manoma a Jihar Neja

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan noma kyauta ga manoma a Jihar Neja

Gwamnatin Tarayya ta fara rabon kayan noma kyauta ga kananan manoma a Jihar Neja domin karfafa noman ko wane lokaci na shekara da kuma bunkasa samar da abinci.

Karamin Ministan Noma da samar da Abinci, Dakta Aliyu Sabi Abdullahi, ya ce wannan shiri wani bangare ne na manufofin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadatar abinci da kuma tsaron abinci a Najeriya.

Kayan da ake rabawa sun hada da taki, magungunan kashe kwari, iri, sinadaran bunkasa amfanin gona, injinan feshi da sauran kayayyakin da za su taimaka wa manoma. Za a ci gaba da raba irin wadannan kayan a jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya.

Ministan ya jinjinawa Gwamnan Jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, bisa nasarorin da jihar ta samu a fannin noma, lamarin da ya ce ya sanya ta zama abin koyi wajen aiwatar da shirye-shiryen gwamnati.

Shi ma Gwamna Bago ya gode wa Shugaba Tinubu bisa tallafin da ya bayar, yana mai cewa shirin zai karfafa gwiwar manoma kuma ya ba su damar dogaro da kansu. Ya kuma bayyana cewa Jihar Neja ta samu damar fitar da irin gyaÉ—a (sesame seeds) na dalar Amurka miliyan 2.2 zuwa kasashen waje, tare da shirin dawo da Bankin Tattalin Arzikin Kananan Manoma (Cooperative Bank) da Naira biliyan 2 domin rage radadin rancen da ke da ruwa mai yawa.


Comment As:

Comment (0)