
Jihar Zamfara
An kashe sojojin Nijeriya biyar a kan hanyar Lilo–Kotorkoshi da ke ƙaramar hukumar Gusau a Jihar Zamfara.
Rundunar Sojin Najeriya ƙarƙashin Operation Fansan Yamma ta tabbatar da mutuwar sojoji biyar a wani kwanton bauna da aka yi a kan hanyar Lilo–Kotorkoshi da ke ƙaramar hukumar Gusau, Jihar Zamfara.
Lamarin ya faru ne a ranar Litinin yayin da dakarun soji ke rakiyar ‘yan kasuwa zuwa kasuwar Gusau. Rahotanni tun da farko sun bayyana cewa an kashe sojoji biyar, yayin da aka hallaka wasu ‘yan bindiga da dama a fafatawar.
A cikin wata sanarwa da aka fitar da yammacin Alhamis, mai magana da yawun rundunar sojin jihar, Kyaftin David Adewusi, ya bayyana cewa dakarun 1 Brigade daga sansanin Forward Operating Base da ke kauyen Lilo sun fuskanci harin ‘yan ta’adda yayin da suke sintiri a yankin Lilo–Kofi.
“A yayin fafatawar mai zafi, dakarunmu sun kashe ‘yan ta’adda shida, wanda hakan ya sa sauran suka gudu cikin ruɗani. Abin takaici, sojoji uku sun rasa rayukansu a wurin, yayin da wasu biyu da suka ji mummunan rauni suka mutu daga bisani,” in ji Adewusi.
Nagarifmradio