
Jihar Kebbi
Yan majalisar tarayya daga jihar Kebbi sun buƙace jami'an tsaro su kama Abubakar malami
Wani rikicin siyasa ya kunno kai a jihar Kebbi bayan ‘yan majalisar tarayya daga jihar suka fito fili suna zargin tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, da yada labarai na karya da suke ganin za su iya jefa jihar da kasa baki daya cikin rudani.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, jagoran Æ´an majalisar, Sanata Adamu Aliero, ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta kama tare da gurfanar da Malami a gaban kotu bisa zargin kokarin tayar da tarzoma da tada hargitsi a jihar.
Sanata Aliero ya ce Malami ya shigo da ‘yan daba daga Sokoto da wasu makwabtan jihohi domin su kai hari kan sakatariyar jam’iyyar APC da ke Birnin Kebbi, lamarin da ya janyo artabu tsakanin magoya bayan Malami da ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar.
Dcl Hausa