Gwamna Idris: Bukin Kifi na Ƙasa da Ƙasa na Argungu Muhimmi ne ga Tattalin Arzikin Ruwa da Cigaban Dorewa

Gwamna Idris: Bukin Kifi na Ƙasa da Ƙasa na Argungu Muhimmi ne ga Tattalin Arzikin Ruwa da Cigaban Dorewa

Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya bayyana Bukin Kifi da Al’adu na Ƙasa da Ƙasa na Argungu a matsayin wata muhimmiyar dama ta samun cigaban dorewa da kuma ƙara kudaden shiga a karkashin tsarin Tattalin Arzikin Ruwa (Blue Economy) na Najeriya.

Gwamna Idris ya bayyana hakan ne a wata takardar gabatarwa mai taken: *“Yawon Buɗe Ido na Kifi da Cigaban Dorewa a Najeriya: Matsaloli, Kalubale da Damar da ke Cikin Bukin Kifi na Argungu”* ga mahalarta Kwasa-Kwasa na Babban Darakta na 47, shekarar 2025, a Cibiyar Kasa ta Tsare-Tsare da Dabaru (NIPSS), Kuru, Jos, Jihar Filato, a ranar Litinin.

An wakilce shi a wajen taron ta Mataimakinsa, Sanata Umar Abubakar Tafida, inda Gwamna Idris ya bayarda tarihin bukin Argungu, yana mai haskaka nasarorin da ya samu da kuma ƙalubalen da ya fuskanta a tsawon lokaci.


Ya shawarci Hukumar Cigaban Yawon Buɗe Ido ta Najeriya (NTDC) da ta haɗa bukin a cikin kalanda na shekara-shekara na yawon buɗe ido na ƙasa, sannan ya bukaci Ma’aikatar Harkokin Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arzikin Kirkire-Kirkire ta Ƙasa da ta gaggauta kammala gine-gine da kayan more rayuwa na filin bukin da aka bari.

Haka kuma, ya bayar da shawarar samar da sabakakkiyar hukuma mai zaman kanta ta hanyar kudirin doka don kula da bukin Argungu. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan hukuma za ta tsara dabarun talla da haɗa kafafen sadarwa na zamani da na gargajiya don ƙara wayar da kai da kuma ganin bukin ya samu karɓuwa a duniya.

Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin sashen kifaye na Najeriya da Ma’aikatar Tattalin Arzikin Ruwa wajen bunkasa tattalin arziki ta hanyar samar da ayyukan yi, yana mai cewa Bukin Argungu wata babbar kafa ce da za ta iya bunƙasa diflomasiyyar al’adu, haɗin gwiwar ƙasashen waje da samun damar kasuwanci.

Ya ƙara da cewa:  
“Wannan dandali yana ba Jihar Kebbi da Najeriya damar jan hankalin al’umma na cikin gida da waje, domin ƙarfafa dangantaka da buɗe ƙofofi zuwa sabon cigaban tattalin arziki.”

 

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)