Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe jagoran ƴan fashin-daji, Babangida Kachalla a jihar Kogi da ke tsakiyar ƙasar.
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe jagoran ƴan fashin-daji, Babangida Kachalla a jihar Kogi da ke tsakiyar ƙasar.
Â
An ruwaito Mai magana da yawun Bataliya ta 12 Laftanar Hassan Abdullahi na cewa lamarin ya faru tun ranar 5 ga watan Satumba a Tunga.
Â
Ya ƙara da cewa mutumin shi ne mataimakin Kachalla Shu’aibu, shugaban wani gungu da ke yawan kai hare-hare a Masallaci-Boka da Dajin Ofere na jihar ta Kogi.
Â
A cewarsa, daga baya kuma sun yi wa wani mai kaiwa ƴanfashin kayayyaki kwanton ɓauna a gadar Agbede–Adankoo, inda suka ƙwace makamai da kayayyaki.
Â
Daga cikin abubuwan da suka samu a hannun ƴanbindigar akwai harsasai, da wayoyin salula 31, da ƙunshin ƙwayoyi, da layu, da tsabar kuɗi ₦16,000.