Anyi Sulhu Tsakanin Al’umma Da Ƴan Bindiga A Faskari, Jihar Katsina

Anyi Sulhu Tsakanin Al’umma Da Ƴan Bindiga A Faskari, Jihar Katsina

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina sun tabbatar da cewa an kulla zaman sasanci tsakanin al’ummar yankin da wasu daga cikin ƴan bindiga da ke addabar yankin tsawon lokaci.

Wannan yarjejeniya ta samu ne a yayin wani zama na musamman da aka gudanar, inda aka cimma matsaya cewa ƴan bindigar za su daina kai hare-hare ko cutar da al’umma, amma za su rika shigowa gari don gudanar da rayuwar yau da kullum cikin lumana.

Wannan mataki ya zo ne bayan dogon lokaci na tashin hankali da kashe-kashe da garkuwa da mutane da aka sha fama da su a yankin, wanda hakan ya tilasta wasu al’umma barin muhallansu.

Yayin da wasu ke kallon wannan mataki a matsayin nasara da ci gaba wajen dawo da zaman lafiya, wasu na nuna damuwa kan amincewa da ’yan bindiga su shiga gari ba tare da an hukunta su ba.

Ana sa ran hukumomi za su ci gaba da sa ido kan yarjejeniyar tare da daukar matakin da ya dace don tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)