
YAN SANDA SUN KAMA MUTANE BIYU DA AKE ZARGI DA SIYAN KAYAN SATA A BIRNIN KEBBI
‘YAN SANDA SUN KAMA MUTANE BIYU DA AKE ZARGI DA SIYAN KAYAN SATA A BIRNIN KEBBI
ANA CIGABA DA NEMAN MAI LAIFI NA GABA
Â
A ranar 11 ga Satumba, 2025, da misalin karfe 2:40 na rana, wani mai suna Architect Usman Wasagu daga unguwar Kawara, Birnin Kebbi, ya kai rahoto a ofishin ‘yan sanda na Divisional da ke Birnin Kebbi cewa a ranar 9 ga Satumba, 2025, da misalin karfe 2:00 na dare, wasu da ba a san ko su wane ba sun fasa shagon sa da ke bayan makarantar Sajo School of Nursing Science, Birnin Kebbi, inda suka sace injuna masu nika kasa guda bakwai (7) na noma (Power Tiller).
Â
Bisa sahihan bayanai da aka samu, wata tawagar ‘yan sanda daga ofishin Divisional na Birnin Kebbi suka dauki mataki cikin gaggawa, inda suka kama mutum biyu: Â
- Hamidu Bagudu, namiji, mai shekaru 52, daga unguwar Tudun Wada Â
- Abdullahi Aliyu, namiji, mai shekaru 35, daga unguwar Nasarawa, dukkansu a Birnin Kebbi.
Â
Â
A binciken farko, sun amsa cewa sun karɓi kayan sata daga wani mai suna Usman Inyamu, daga Tudun Wada, wanda yanzu haka yana tsere. Sun kara da cewa, Usman ya sayar da injunan ga Abdullahi Aliyu kan kudi Naira miliyan daya da dubu dari takwas da arba'in (#1,840,000.00), daga cikin kudin an kwato Naira dubu dari biyu da hamsin (#250,000.00) a matsayin shaida.
Â
Haka kuma, ‘yan sanda sun samu nasarar kwato duka injuna bakwai (7) da aka sace.
Â
Saboda wannan nasara da aka samu, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kebbi, CP Bello M. Sani, ya yabawa DPO na Birnin Kebbi da tawagarsa bisa kwarewa da saurin daukar mataki. Ya kuma jaddada kudirin rundunar wajen kawar da duk wasu laifuka masu tayar da hankali a jihar Kebbi.
Â
Kwamishinan ya umurci a tura wannan shari’a zuwa Sashen Binciken Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Â
CP Bello M. Sani ya kara jaddada cewa, idan al’umma za su rika bayar da sahihan bayanai cikin lokaci, rundunar za ta tabbatar da cewa babu wuri ga masu aikata laifi a jihar Kebbi.
Nagarifmradio