
Yan bindiga sun yi wa wani hakimi yan kan rago a Zamfara
Wasu ƴanbindga ɗauke da makamai sun auka wa garin Dogon Daji da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, tare da yi wa hakimin garin yankan rago.
Shugaban ƙaramar hukumar Tsafe Hon. Garba Shehu Tsafe ya tabbatar wa BBC cewa lamarin ya faru ne a yau Litinin da maraice.
''Yanzu-yanzu muka samun rahoton cewa Æ´anbindiga sun shiga garin Dogon Daji na Nasarawar Keta, sun kuma yanka hakimin garin'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa a wunin yau ƴanbindigar sun tare wasu hanyoyi a yankin da ke kai wa zuwa Gusau.
Shugaban ƙaramar hukumar ya alaƙanta ƙaruwar hare-haren yankin da sluhun da ake yi a jihar Katsina mai makwabtaka.
Dama dai masana tsaro sun jima suna gargaÉ—in cewa yin sulhu da Æ´anbindigar ba mafita ba ce, saboda za su iya barin wurin da aka yi sulhu da su domin kai hari wasu yankunan, sannan su dawo wurin da aka yi sulhun domin samun mafaka.
BBC