Aliko Ćangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maĆarĆashiya domin kashe matatarsa
- By NAGARIFMNEWS --
- Tuesday, 16 Sep, 2025

- 86 views
Mai kuÉin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ćangote, Alhaji Aliko Ćangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maĆarĆashiya domin kashe matatarsa.
Ćangote ya yi zargin cewa miyagun âyan kasuwan suna ĆoĆarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masanaâantar tufafi ta Ćasar.
Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara Éaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da Ćalubale tun daga farko.
Ya ci gaba da cewa, âAmma abin da muka yi shi ne mun sa Najeriya da nahiyar Afirka gaba Éaya su yi alfahari.â
Ćangote ya ce matatar ta riga ta fitar da lita biliyan 1.8 na man fetur zuwa Ćasashen waje cikin watanni uku da suka gabata, sannan tana da isasshen Ćarfi wajen cika buĆatar cikin gida.
Ya ce tun daga fara aikin matatar a watan Satumbar 2024, dogayen layukan man fetur da suka fi shekaru 50 ana fama da su a Najeriya sun zama tarihi.
Ćangote ya Ćara da cewa farashin fetur ya sauka daga kusan Naira 1,100 zuwa N841 a wasu jihohi, kuma da zarar sabbin motocin gas (CNG) masu dakon mai sun fara aiki a duk faÉin Ćasar, rage farashin zai fi tasiri.
Ya kuma bayyana cewa sabbin motocin CNG 4,000 za su samar da aĆalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran maâaikata.
Ćangote ya zargi masu harkar mai da haÉa kai da âyan kasuwa na cikin gida da na waje da ĆoĆarin hana nasarar matatar.
A kan zargin cewa bai wadatar da Ćasa da fetur ba, sai ya mayar da martani da cewa: âIdan ba mu da Ćarfin samar da mai, me ya sa muke fitarwa zuwa Ćasashen waje?â
Ya kuma yi baâa ga Ćungiyar Maâaikatan Mai (NUPENG) wadda ta ce rage farashin fetur na matatar Dangote âkyautar Girka ce.â Dangote ya ce: âKo da kuwa kyautar Girka ce, ai kyauta ce, za ta kuma ci gaba da kasancewa.â
Nagarifmradio




