Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa

Mai kuɗin Afrika kuma Shugaban Matatar Mai ta Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya zargi wasu manyan masu harkar mai da shirya maƙarƙashiya domin kashe matatarsa.

Ɗangote ya yi zargin cewa miyagun ’yan kasuwan suna ƙoƙarin kashe matatar mansa mai darajar dala biliyan 20, kamar yadda aka kashe masana’antar tufafi ta ƙasar.

Ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Legas yayin bikin cika shekara ɗaya da fara samar da fetur a matatar, inda ya ce tafiyar ta kasance cike da ƙalubale tun daga farko.

Ya ci gaba da cewa, “Amma abin da muka yi shi ne mun sa Najeriya da nahiyar Afirka gaba ɗaya su yi alfahari.”

Ɗangote ya ce matatar ta riga ta fitar da lita biliyan 1.8 na man fetur zuwa ƙasashen waje cikin watanni uku da suka gabata, sannan tana da isasshen ƙarfi wajen cika buƙatar cikin gida.

Ya ce tun daga fara aikin matatar a watan Satumbar 2024, dogayen layukan man fetur da suka fi shekaru 50 ana fama da su a Najeriya sun zama tarihi.

Ɗangote ya ƙara da cewa farashin fetur ya sauka daga kusan Naira 1,100 zuwa N841 a wasu jihohi, kuma da zarar sabbin motocin gas (CNG) masu dakon mai sun fara aiki a duk faɗin ƙasar, rage farashin zai fi tasiri.

Ya kuma bayyana cewa sabbin motocin CNG 4,000 za su samar da aƙalla ayyukan yi 24,000, ciki har da direbobi, makanikai da sauran ma’aikata.

Ɗangote ya zargi masu harkar mai da haɗa kai da ’yan kasuwa na cikin gida da na waje da ƙoƙarin hana nasarar matatar.

A kan zargin cewa bai wadatar da ƙasa da fetur ba, sai ya mayar da martani da cewa: “Idan ba mu da ƙarfin samar da mai, me ya sa muke fitarwa zuwa ƙasashen waje?”

Ya kuma yi ba’a ga Ƙungiyar Ma’aikatan Mai (NUPENG) wadda ta ce rage farashin fetur na matatar Dangote “kyautar Girka ce.” Dangote ya ce: “Ko da kuwa kyautar Girka ce, ai kyauta ce, za ta kuma ci gaba da kasancewa.”

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)