Jihar Kebbi

Gwamna Idris ya rantsar da sabon Kwamishina, ya ƙaddamar da Hukumar Raya Ma’adanai

Gwamna Idris ya rantsar da sabon Kwamishina, ya ƙaddamar da Hukumar Raya Ma’adanai

Gwamnan Jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), ya rantsar da Hon. Garba Hassan Warrah a matsayin sabon Kwamishinan Raya Ma’adanai da Ma’adinai.

Haka kuma, Gwamnan ya ƙaddamar da sabuwar Hukumar Raya Ma’adanai ta Jihar Kebbi, tare da naɗa Abdullahi Buhari Warrah a matsayin Darakta Janar na hukumar.

Sabon Kwamishinan, Hon. Garba Hassan Warrah, ya maye gurbin Alhaji Haliru Aliyu Muhammad Wasagu, wanda Gwamnan ya dakatar.

An gudanar da rantsarwar ne a ranar Litinin, a Fadar Gwamnati da ke Birnin Kebbi, inda Babban Alkalin Jihar, Mai Shari’a Umar Abubakar, ya gabatar da rantsuwar a gaban Gwamna Nasir Idris.

Gwamna Idris ya taya sabbin jami’an murna, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin tarihi. Ya ce an zaɓe su ne bisa cancanta da tarihin aiki, kuma gwamnatinsa ba za ta lamunci sakaci ko rashin aiki daga wani jami’i ba.

“Ina da yakinin nagartar ku, shi yasa muka ba ku wannan nauyi. Amma idan kuka kasa, za mu sallame ku,” in ji Gwamnan.

Ya jaddada cewa babban aikin sabon kwamishinan da hukumar ita ce haɓaka kuɗaɗen shiga ga jihar.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)