Yajin aikin sai baba-ta-gani da ƙungiyar likitocin masu neman ƙwarewa na reshen Abuja, babban birnin Najeriya ta fara tasiri a wasu asibitocin birnin.

Yajin aikin sai baba-ta-gani da ƙungiyar likitocin masu neman ƙwarewa na reshen Abuja, babban birnin Najeriya ta fara tasiri a wasu asibitocin birnin.
 
Yajin aikin, wanda ya shiga rana ta biyu a jiya Talata, ya gurgunta ayyuka a wasu daga cikin asibitocin, da kuma cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko a birnin.
 
Wannan ya biyo bayan cikar wa’adin yajin aikin gargaɗi na mako guda da ƙungiyar ta ARD ta gindaya wa gwamnatin a kan ta biya musu buƙatunsu.
 
An ruwaito ganin marasa lafiya a asibitin Maitama a cikin wani hali sakamakon rashin likitoci a asibitin.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)