
Yan Bindiga Sun Nemi A Gina Musu Makarantu, Asibitoci Da Filayen Kiwo a Matsayin Yarjejeniyar Sasanci
Yan Bindiga Sun Nemi A Gina Musu Makarantu, Asibitoci Da Filayen Kiwo a Matsayin Yarjejeniyar Sasanci,” Inji Gwamnatin Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ’yan bindiga da ke sassan jihar sun gabatar da wasu buƙatu a yayin tattaunawar zaman lafiya da al’ummomin yankunan jihar.
Kwamishinan Tsaro na jihar, Nasiru Mu’azu ne ya shaida wa BBC Hausa cewa cikin buƙatun akwai a gina makarantu, a gina asibitoci, da kuma samar da filayen kiwo ga makiyaya.
A cewarsa, ba gwamnatin Katsina bace ta fara tattaunawa da ’yan bindigar, Ra'ayin shugabannin al’umma a ƙananan hukumomin Dan Musa, Jibiya, Batsari, Kankara, Kurfi da Musawa ne, da suka nemi hanyar sulhu don kawo ƙarshen kashe-kashe, satar shanu da garkuwa da mutane da aka dade ana fama da su.
Mu’azu ya bayyana cewa rushewar shirin afuwar da gwamnatin baya ta aiwatar ne ya taɓarɓare lamarin tsaro, inda hare-haren suka yawaita daga ƙananan hukumomi guda 5 tsakanin 2011 da 2015 zuwa shekarar 2023.
Rahoton kamfanin bincike na tsaro, Beacon Consulting, ya nuna cewa a watannin farko na 2025 kaɗai, mutane 341 aka kashe, 495 kuma aka sace a hare-hare 247 da suka auku a Katsina.
A watan Yuli da ya gabata, gwamnatin jihar ta sanar da sabon shiri na gyara da kuma koya wa ’yan bindiga da suka ajiye makamai ilimin addini da na zamani, tare da horo a sana’o’i, domin su sake komawa cikin al’umma ba tare da cutarwa ba.
Sai dai makon da ya gabata, gwamnati ta gudanar da babban taro domin nazarin halin tsaro a jihar. An tabbatar cewa gwamnati za ta yi ƙoƙari wajen cika wasu daga cikin buƙatun ’yan bindigar domin a samu dawwamammen zaman lafiya.
BBC