Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 10 a sobon hatsarin jirgin ruwa a Sokoto

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Jihar Sokoto DSP Ahmed Rufai, ya tabbatar wa manema labarai cewa mutanen sun nutse a cikin kogi a yankin ƙaramar hukumar Sabon Birni yayin da suke tserewa daga hare-haren da 'yan bindiga suka kai ƙauyen Zalla Bango a ƙarshen mako.

Sai dai kawo yanzu hukumomin agaji ba su tabbatar da adadin mutanen da lamarin ya shafa ba, amma rahotanni na cewa adadin ka iya zarta wanda 'yan sanda suka bayar.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)