Gwamnatin Kebbi Ta Mayar da Sashen Haihuwa na Fati Lami Zuwa Sabon Gini a Asibitin Sir Yahaya Memorial

Gwamnatin Kebbi Ta Mayar da Sashen Haihuwa na Fati Lami Zuwa Sabon Gini a Asibitin Sir Yahaya Memorial

Gwamnatin Jihar Kebbi ta koma da sashen haihuwa na Fati Lami zuwa wani sabon gini mai fadi da dacewa a cikin Asibitin Sir Yahaya Memorial da ke Birnin Kebbi, domin inganta kula da lafiyar mata da kuma samar da yanayi mai kyau ga ma'aikatan lafiya.

Wannan sauyin wuri ya zo ne bisa umarnin Gwamna Nasir Idris, a matsayin wani bangare na kokarinsa na gyara fannin lafiya da kuma tabbatar da ingantattun ayyukan lafiya a fadin jihar.

A yayin rangadi da aka kai zuwa tsohon da sabon ginin, Babban Darakta kuma Sakatare Dindindin na asibitin, Dr. Shehu Koko, ya bayyana cewa yawan jama'a da karuwar marasa lafiya daga wasu asibitoci sun fi karfin tsohon sashen haihuwa.

Ya ce tsohon ginin na fama da matsaloli kamar karancin gado da karancin wuri, wanda ke hana ma’aikata aiki yadda ya kamata. Sabon ginin kuma yana da karin gado, babban dakin haihuwa, da kuma damar yin tiyata biyu a lokaci guda — wanda hakan zai taimaka matuka wajen inganta kula da mata masu juna biyu.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)