Wata kotun soji a Najeriya ta yanke wa sojoji huɗu hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ƙa’ida ba, a Maiduguri, jihar Borno.
Wata kotun soji a Najeriya ta yanke wa sojoji huɗu hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ƙa’ida ba, a Maiduguri, jihar Borno.
Â
A cikin wata sanarwa da kotun ta fitar, shugaban Kotun, Brigadier-Janar Mohammed Abdullahi, ya bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huÉ—u hukuncin É—aurin rai-da-rai, yayin da aka É—aure mutum É—aya shekaru 15 a gidan yari.
Â
Wannan hukunci ya biyo-bayan amincewar su kan aikata laifuffukan da suka haɗa da "sata da kasuwancin makamai ba bisa ƙa’ida ba, da taimaka wa maƙiya", wanda duka laifuka ne ƙarƙashin dokar sojojin Najeriya.
Â
Kotun ta bayyana cewa "irin wannan safarar da ba bisa ƙa’ida ba na zamewa haɗari ga sojoji da ayyukan soja, da kuma tsaron ƙasa; don haka, yana nufin taimaka wa maƙiyan ƙasar".
Â
Shugaban Kotun, Brigadier-Janar Abdullahi, ya ce waɗannan laifuka da sojojin suka aikata ba matsala ce kawai ta karya doka ba, har ma da cin amana, da martabar da ake sa ran sojoji su riƙe.




