Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka na Patigi a Jihar Kwara, inda suka kashe wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane.

'Yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka na Patigi a Jihar Kwara, inda suka kashe wata mata mai juna biyu tare da wasu mutane.

Haka kuma sun yi garkuwa da mutane takwas tare da jikkata da dama.

Shaidu sun ce maharan sun shiga ƙauyukan ne a babura, inda suka dinga harbi ba ƙaƙƙautawa wanda ya sa mazauna ƙauyukan suka gudu.

Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Motokun, Egboro da Fanagun.

Wani mai suna James Ibrahim, ya ce: “Mun farka da safe muka ga mutane suna gudu daga Motokun bayan harin. An harbi wata mace wadda daga bisani ta rasu a asibitin Patigi.

“Sun kuma sace mutum takwas tare da yin awon gaba da babura da dama. Muna roƙon gwamnati ta taimake mu.”

Wani shugaban al’umma, Malam Mohammed, ya ƙara da cewa: “’Yan bindigar sun fara kai hari Motokun, daga nan suka nufi Egboro. Yawancin mazauna ƙauyukan sun tsere.

“Sun kashe wani malami da ya saba zuwa yin wa’azi, sannan suka sace mutanen da suke ganin za su iya karbar fansa a hannunsu.”

Harin ya tilasta wa magidanta da dama barin gidajensu, inda suka nemi mafaka a garuruwan da ke kusa da su.

Mazauna ƙauyukan sun ce suna rayuwa cikin tsoro saboda hare-haren da ke ƙara yawaita kullum.

Gwamnatin Jihar Kwara, ta yi alƙawarin ƙara tsaurara tsaro tare da buƙatar al’umma su fallasa masu bai wa ’yan bindiga bayanai.

Rundunar sa-kai da sojoji kuma sun ƙara tsaurara tsaro, duk da cewa jama’a sun koka cewa sau da yawa maharan na kai farmaki kafin a kai musu agaji.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)