Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025.
Gwamnatin Tarayya ta umarci dukkanin ma’aikatu, hukumomi, sojoji da kuma cibiyoyin kuɗi da ma’aikatu masu zaman kansu da su fara tantance takardun shaidar kammala makaranta na ma’aikatansu daga ranar 6 ga watan Oktoba, 2025.
Wannan mataki ya biyo bayan yawaitar bogi da takardun karatu na bogi a Najeriya.
Za a yi tantancewar ne ta hanyar tsarin amfani da kwamfuta mai suna Nigeria Education Repository and Databank (NERD), wanda aka ƙirƙiro domin adanawa da tabbatar da sahihancin takardun karatun ma’aikata.
A wannan tsari, babu wanda za a ɗauka aiki ko a tabbatar masa da muƙami sai an tabbatar da takardunsa ta hanyar National Credential Verification Service (NCVS).
Kowace takarda da aka tabbatar za a ba ta wata lamba ta musamman mai tsaro.
Jami’ai sun ce wannan mataki zai kare mutuncin ilimi a Najeriya, kodayake masana sun yi gargaɗin cewa wasu za su iya rasa ayyukansu.
A baya, an gano ’yan Najeriya da dama suna amfani da takardun bogi don samun aiki ko ƙarin matsayi a wajen aiki.
A shekarar 2024, gwamnati ta soke takardun shaidar kammala karatu sama da 22,000 daga jami’o’in bogi na Jamhuriyar Benin da Togo.
Haka kuma, gwamnati ta umarci cibiyoyi su riƙa gabatar da rahoton bin doka duk shekara domin tabbatar da tsauraran matakai.
Wannan zai sa ya zama da wuya a riƙa yin amfani da takardun ƙarya ba tare da an gano su ba.
Masana ilimi sun ce idan aka aiwatar da tsarin yadda ya kamata, zai dawo da mutuncin takardun shaidar kammala karatu na Najeriya a idon duniya, tare da bai wa É—alibai na gari damar samun aiki.
Nagarifmradio




