Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sanya la’adar Dala 10,000, kwatankwacin Naira miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran.

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sanya la’adar Dala 10,000, kwatankwacin Naira miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran.

Ana dai neman Olumide ne a Amurka ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan zamba da dama.

A cewar sanarwa da aka wallafa a shafin FBI a ranar Laraba, ana tuhumar shi da laifukan zamba a banki, zamba da takardun shaida, laifukan da ake zargin ya aikata a jihar Illinois tun shekarar 2001.

Adediran, mai shekaru 56, yana amfani da sunaye daban-daban kamar Kevin Olumide Adediran, Eric O. Williams, Maxo Alexandre, Olumide Adkins, da Edward N. Anderson.

Ana zargin ya yi ƙoƙarin cire kuɗi daga takardun banki na bogi da kuma amfani da bayanan sirri na ’yan ƙasar Amurka da aka sace don buɗe asusun banki da na katin bankin.

FBI ta ce Olumide ya tsere daga jihar Illinois a ƙarshen Disamban 2001, kafin fara shari’arsa.

FBI ta ce, “FBI za ta bayar da lada har zuwa Dala $10,000 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama da hukunta Olumide Adebiyi Adediran.”

FBI ta bukaci duk wanda ke da bayani kan inda yake da ya tuntubi ofisoshinta a Amurka ko ofishin jakadancin Amurka mafi kusa da shi.

Aminiya

Comment As:

Comment (0)