A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, Collins zai shiga sahun tarihin duniya yayin da zai yi ƙoƙarin kafa tarihi har guda biyu na shiga kundin ‘Guinness World Record’ a fannin zanen fuska.
A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, Collins zai shiga sahun tarihin duniya yayin da zai yi ƙoƙarin kafa tarihi har guda biyu na shiga kundin ‘Guinness World Record’ a fannin zanen fuska.
Kamfanin Indomie ne zai tallafa wa É—alibin domin gwada bajintarsa wajen shiga kundin Guinness World Record.
A wajen ɗalibin na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, zane ba kawai sha’awa ba ce kaɗai, face hanya ta shiga kundin tarihin duniya.
Burinsa shi ne zana fuskar mutane 12 ko sama da haka a cikin minti uku da kuma fuskar mutane 220 ko sama da hakan cikin sa’a guda, inda yake ƙoƙarin ƙwace kambun da Emilia Zakonnova, wadda ke riƙe da shi, wadda ta zana fuskar mutane 12 cikin minti 3 a ranar 30 ga watan Yuli, 2025.
Ya taɓa gwada irin wannan a shekarar 2024 ammabai kai gayin nasara ba, wannan yasa ya ƙara himma da ƙaimi don gwada sa’arsa.
“Na koyi darusa da yawa daga yunƙurina na farko. Yanzu na shirya, na mayar da hankali kuma na ƙuduri aniyar cimma nasara
Nagarifmradio