Jihar Kebbi
Gwamna Idris Ya Umurci Jamiâan Tsaro Su Karbi Filin HaĆar Zinare a Karamar Hukumar Yauri.
- By NAGARIFMNEWS --
- Thursday, 25 Sep, 2025

- 298 views
Gwamna Idris Ya Umurci Jamiâan Tsaro Su Karbi Filin HaĆar Zinare a Karamar Hukumar Yauri.
Gwamnan Jihar Kebbi, Comrade Dr Nasir Idris, ya umurci jamiâan tsaro da su karbi filin haĆar zinare na shirin raya masanaâantar haĆar zinare na shugaban Ćasa (PAGIM) a Karamar Hukumar Yauri, har sai an daidaita ayyukan filin a cikin hukumance tare da Maâaikatar HaĆa da Maâadanai ta Jihar.
Ya bayar da wannan umarni a ranar Alhamis yayin wani ziyarar duba filin, bayan rikicin da ya faru a baya-bayan nan tsakanin masu aikin hannu da kamfanin (PAGIM), wanda ya yi sanadin mutuwar mutum Éaya.
Gwamnan ya umurci a dakatar da duk wani aiki na haĆar maâadinai a halin yanzu, har sai an daidaita lamarin kuma aka dawo da zaman lafiya a yankin.
Wannan, a cewarsa, yana da nufin tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya don amfanin alâummar yankin da kuma jamaâa baki Éaya.
âJamiâan tsaro su dauki nauyin yankin gaba Éaya, kuma ina roĆon duk masu aikin hannu da su yi rajista a hukumance tare da hukumomin da abin ya shafa don guje wa duk wani rikici ko tauye zaman lafiya a yankin,â in ji shi.
Gwamnan ya kuma bukaci matasan yankin da su rungumi tattaunawa, ta yadda za a iya warware duk wani rashin jituwa cikin lumana, yana mai cewa babu alâumma da za ta ci gaba a cikin hargitsi, rashin jituwa, ko tauye zaman lafiya.
Yayin da yake Ćarfafa matasan da su ji dadin zaman lafiya da haÉin kai a tsakaninsu, Dr Idris ya gargadi su da su guji duk abin da zai iya haifar da rikici, Ćiyayya, ko rarrabuwar kawuna a tsakaninsu.
Filin haĆar maâadin, wanda ke a Maraba Yauri a Karamar Hukumar Ngaski ta jihar, ya kasance wurin da masu aikin hannu ke samun riba mai yawa.
A martaninsa, shugaban kamfanin, Musa Dantata, ya danganta rikicin da rashin bin Ćaâidodin da suka dace, yayin da ya roĆi Gwamnan Jihar Kebbi da ya umurci duk masu haĆar maâadinai da su yi rajista a hukumance tare da hukumomin da abin ya shafa.
Ta hanyar yin rajista da hukumomin da abin ya shafa, in ji shi, ba kawai za a iya shawo kan rikici ba, har ma za a ji dadin bin Ćaâidodi.




