yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Yandoto, ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka halaka mutum biyar yayin da ake sallar asuba a safiyar Juma’a.

Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci da ke kauyen Yandoto, ƙaramar hukumar Tsafe, inda suka halaka mutum biyar yayin da ake sallar asuba a safiyar Juma’a.

Daily Trust ta rawaito cewa shaidun gani da ido sun ce maharan sun kutsa cikin masallacin ne suka fara harbi ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar nan take tare da jikkata wasu da dama.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)