Helkwatar yan sandan Abuja

An sace Motar 'yan sanda a Helkwatar 'yan sanda ta kasa dake Abuja.

An sace Motar 'yan sanda a Helkwatar 'yan sanda ta kasa dake Abuja.

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja sun tabbatar da cewa wata motar jami’an ƴan sanda ta ɓace daga harabar Hedikwatar ƴan Sanda ta Ƙasa.

Wata majiya daga cikin rundunar ta bayyana cewa motar, wacce take cikin jerin motocin aiki na ofisoshin rundunar, ta ɓace ne cikin yanayi mai cike da ɗaukar hankali, kuma hukumomi sun fara bincike domin gano yadda aka yi garkuwa da ita.

Rundunar ƴan sanda ta ƙasa ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa an ɗauki duk matakan bincike da tsaro domin gano motar da kuma kama wadanda suka yi garkuwa da ita.An sace Motar 'yan sanda a Helkwatar 'yan sanda ta kasa dake Abuja.

 

Rariya news

Comment As:

Comment (0)