Gwamnan Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta biya ‘yan kwangila ‘yan asalin jihar da ke da takardun kwangila na gaskiya, ba tare da la’akari da jam’iyyar da suka fito ba.

Gwamnan Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya tabbatar da cewa gwamnati za ta biya ‘yan kwangila ‘yan asalin jihar da ke da takardun kwangila na gaskiya, ba tare da la’akari da jam’iyyar da suka fito ba.

Gwamnan ya ce bashin da gwamnatin da ta gabata ta bar wa waɗannan ‘yan kwangila za a biya su a hankali don ƙarfafa musu gwiwa.

Ya bayyana hakan ne yayin da shugabannin ƙungiyar ‘Yan Kwangila ‘Yan Asalin Jihar suka kai masa ziyarar girmamawa a fadar gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Litinin.

Ya ce:  
*"Da ikon Allah, zan yi iyaka kokarina wajen biyan bashin da ake bin ku, har da wanda gwamnatin da ta gabata ta bari, matuƙar kuna da takardu na gaskiya da ke nuna hakan. Kowane ɗan kwangila na gida za a kula da shi ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba. Ina so in jaddada cewa ina ba da fifiko ga ‘yan kwangila na cikin gida kuma zan ci gaba da yin hakan.

Ina amfani da wannan dama in gode muku bisa goyon bayan da kuka bani tun daga lokacin zaɓe har zuwa yanzu. Wannan jiha taku ce, gwamnati kuma taku ce, ita ce gwamnatin jama’a, daga jama’a kuma don jama’a.

 

Gwamnan ya bayyana cewa bai wa ‘yan kwangila na gida kwangila zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa da dama a fadin jihar da kuma ƙara inganta tsaro.

 

Tun da farko, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Nayaya Nachiso Ambursa, ya gode wa gwamna bisa damar da ya ba su su nuna ƙwarewarsu da fasahar su wajen aiwatar da ayyuka.

 

Ya tabbatar wa da gwamnan cewa za su yi iya ƙoƙarinsu wajen ganin sun kammala ayyuka yadda ya kamata da kuma a cikin lokacin da aka kayyade.

 

Sai dai, shugaban ya roki gwamnatin da ta ci gaba da basu goyon baya, musamman wajen saurin biyan su kudaden kwangila domin su kammala ayyuka cikin lokaci.

 

‘Yan kwangilar sun kuma yi alkawarin mara wa gwamnatin Kauran Gwandu baya don ganin an cimma burin samun wa’adin mulki na biyu

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)