Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan Ƙwadago na Najeriya, Mohammed Dingyaɗi a jiya Litinin.

Ƙungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin iskar Gas da Man fetur, PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin-aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Man Ɗangote.
 
Ɓangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi ƙarƙashin jagorancin Ministan Ƙwadago na Najeriya, Mohammed Dingyaɗi a jiya Litinin.
 
A jiya Litinin ne ƙungiyar PENGASSAN ta shiga yajin-aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Ɗangote na korar wasu ma'aikatanta kimanin 800.
 
Babu dai wata sanarwa daga ɓangaren Matatar Dangote bayan tattaunawa da ƙungiyar PENGASSAN; amma a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, ta ce ta sallamar ma'aikatan ne a wani mataki na ƙoƙarin daidaita tsarin aikin matatar.
 
Matatar Ɗangote ta kuma bayyana matakin yajin-aikin PENGASSAN a matsayin rashin aiki da doka, da ƙoƙarin zagon-ƙasa ga Najeriya da al'ummarta.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)