Æangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi ÆarÆashin jagorancin Ministan Æwadago na Najeriya, Mohammed DingyaÉi a jiya Litinin.
Æungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin iskar Gas da Man fetur, PENGASSAN ta ce tana nan kan bakarta na ci gaba da yajin-aiki bayan kasa samun maslaha tsakaninta da matatar Man Æangote.
Â
Æangarorin biyu sun tashi baran-baran a tattaunawar da suka yi ÆarÆashin jagorancin Ministan Æwadago na Najeriya, Mohammed DingyaÉi a jiya Litinin.
Â
A jiya Litinin ne Æungiyar PENGASSAN ta shiga yajin-aiki na sai baba ta gani saboda matakin matatar Æangote na korar wasu ma'aikatanta kimanin 800.
Â
Babu dai wata sanarwa daga Éangaren Matatar Dangote bayan tattaunawa da Æungiyar PENGASSAN; amma a sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, ta ce ta sallamar ma'aikatan ne a wani mataki na ÆoÆarin daidaita tsarin aikin matatar.
Â
Matatar Æangote ta kuma bayyana matakin yajin-aikin PENGASSAN a matsayin rashin aiki da doka, da ÆoÆarin zagon-Æasa ga Najeriya da al'ummarta.




