Yan bindiga a Jihar Zamfara sun kwace wayoyin wasu ’yan sanda tare da sace wasu kansiloli biyu da kuma wani liman a yayin wani gagarumin hari da suka kai a unguwar Tsauni da ke Gusau, babban birnin jihar.

’Yan bindiga a Jihar Zamfara sun kwace wayoyin wasu ’yan sanda tare da sace wasu kansiloli biyu da kuma wani liman a yayin wani gagarumin hari da suka kai a unguwar Tsauni da ke Gusau, babban birnin jihar.

Shugaban ƙaramar hukumar Maradun, Hon. Sanusi Gama Giwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa kansilolin da aka sace ’yan majalisar sa ne.

An sace kansilolin biyu ne waɗanda ke wakiltar mazaɓar Gidan Goga da kuma Tsibiri a ƙaramar hukumar da misalin ƙarfe 8:05 na dare a kusa da wani ofishin ’yan sanda, jim kaɗan bayan sun idar da sallar a wurin.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)