Dangote

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin zaman sasantawa da aka shiga tsakanin Kamfanin Matatar Dangote da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN kan rikicin da ya kunno kai sakamakon korar ma’aikata da kamfanin ya yi, Dangote ya zaɓi biyan ma'aikatan albas

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin zaman sasantawa da aka shiga tsakanin Kamfanin Matatar Dangote da ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN kan rikicin da ya kunno kai sakamakon korar ma’aikata da kamfanin ya yi, Dangote ya zaɓi biyan ma'aikatan albashin shekara biyar kyauta maimakon mayar da su aiki.

Majiyoyin sun tabbatar wa Jaridar Premium Times cewa Dangote Refinery ta yi tayin biyan albashin ma’aikatan da aka kora na tsawon shekaru biyar ba tare da yin wani aiki ba, saboda tsoron ɓarnar da yake zargin za su iya haifar masa a matatar idan suka ci gaba da zama.

Majiyar ta ce Dangote ya yi masu wannan tayi ne a lokacin da ake tattaunawar, wanda ya ce hakan zai bai wa ma’aikatan damar neman wasu ayyuka daban a yayin da suke zaune a gida suna ci gaba da karɓar albashinsu kowane wata tsawon shekaru biyar.

Majiyoyin sun ce duk da cewa wakilan gwamnati sun nuna damuwa kan yawan kuɗin da kuma asarar da kamfanin zai iya yi, matatar Dangote ta dage cewa gara yin wannan asarar da barin ma’aikatan su ci gaba da shiga cikin matatar.

Nahiyoyi

Comment As:

Comment (0)