Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, sashen Kamba, ta hallaka wasu da ake zargin ‘yan fashi ne na Lakurawa guda uku a yayin musayar wuta a karamar hukumar Dandi.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi, sashen Kamba, ta hallaka wasu da ake zargin ‘yan fashi ne na Lakurawa guda uku a yayin musayar wuta a karamar hukumar Dandi.

 

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta sashen Kamba ta hallaka wasu da ake zargin ‘yan fashi ne na Lakurawa guda uku a yayin musayar wuta mai zafi a karamar hukumar Dandi.

 

A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ya fitar wa manema labarai a ranar Juma’a, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wani gungun ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Gorun Yamma.

 

“Bayan samun sahihan bayanan sirri, DPO na Kamba, SP Mohammed Bello Lawal, ya jagoranci hadakar jami’an ‘yan sanda da masu sa kai zuwa wajen da abin ya faru.

 

“Rundunar tsaro ta yi artabu da ‘yan bindigar cikin doguwar musayar wuta, inda aka kashe mutane uku daga cikinsu, yayin da wasu suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga.”

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)