Rashin tsaro Sokoto da Kebbi

Mutane a Sokoto Na Neman Taimako Saboda Ƙaruwar Hare-Haren Ƴan Bindiga

Mutane a Sokoto Na Neman Taimako Saboda Ƙaruwar Hare-Haren Ƴan Bindiga

A wasu yankuna na Sokoto kamar Kebbe, Isa da Sabon Birni, ƴan bindiga sun addabi mutane. Ana kashe mutane, ana ƙona gidaje, kuma mutane da dama sun gudu daga ƙauyukansu. Wasu ba su da inda za su zauna, ba su da abinci, ba su da tsaro.

Shugabannin yankin sun roƙi gwamnati ta ba su damar mallakar makamai don kare kansu. Sun ce gwamnati ta ba su kuɗi kai tsaye don su iya samar da tsaro a ƙasa. “Idan gwamnati ba za ta kare mu ba, to ta bar mu mu kare kanmu,” in ji wani shugaba.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ba da tallafi – naira miliyan 293 da buhunan abinci fiye da 2,500. Ya ce za a kafa dokar hukunta masu taimaka wa ƴan bindiga da bayanai. Ya kuma raba motoci 180 don taimaka wa jami’an tsaro. Amma mutane na ganin hakan bai isa ba.

A Kebbe kaɗai, ƙauyuka 12 sun zama kufai. Manoma sun daina zuwa gona, kasuwanni sun rufe, rayuwa ta ƙara wahala.

Wannan matsala ba ta tsaya Sokoto kaɗai ba – ta yadu a arewacin Najeriya. Mutane na cikin tsoro, suna neman taimako, suna fatan zaman lafiya ya dawo.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)