Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Bindiga, Kachalla Maidawa, da Wasu 35..
Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Bindiga, Kachalla Maidawa, da Wasu 35..
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Kachalla Maidawa, tare da mutane 35 daga cikin tawagarsa a jerin hare-haren da suka ɗauki mako ɗaya a jihohin Arewa maso Yamma.
Wata sanarwa daga rundunar Defence Headquarters (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun gudanar da samame a wurare da dama ciki har da Katsina, Zamfara, Kaduna da Sokoto, inda suka lalata maboyar ‘yan ta’adda, suka kwato bindigogi da motocin yaki.
“An kashe Kachalla Maidawa, wanda ya jima yana addabar al’umma da sace-sacen mutane, fashi da kashe-kashe. Rundunar ta kuma kama wasu daga cikin mabiyansa da dama,” in ji DHQ.
Rahotanni sun ce Kachalla Maidawa yana ɗaya daga cikin manyan shugabannin ‘yan bindiga da ke da alaƙa da ISWAP da sauran ƙungiyoyin ta’addanci, kuma an daɗe ana nema saboda hare-haren da suka kashe daruruwan mutane a yankin.
Sojojin sun bayyana cewa za su ci gaba da bincike da sintiri a dazukan Arewa maso Yamma, tare da nufin kare rayukan al’umma da dawo da zaman lafiya.
“Ba za mu tsaya ba har sai mun tabbatar da cewa babu wani wuri da ‘yan ta’adda ke samun mafaka,” in ji kakakin rundunar.
Nagarifmradio




