Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba.

Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da hannu wajen sace Hakimin Garin Garun-Babba, Alhaji AbdulMumini Mudi Zakari, a shekarar 2023.
 
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce an kama wanda ake zargin, mai suna Usman Lawan Baba, wanda aka fi sani da “Yellow” - mai shekara 27, a ranar 2 ga watan Oktoba, 2025, a garin Dakatsalle da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji.
 
Wanda ake zargin, tare da wasu, sun sace Hakimin sannan suka ƙwace masa kuɗi har Naira miliyan 2.75, da waya ƙirar Tecno Kevo-4, da kuma agogo. Sai dai, daga baya ƴansanda sun ceto Hakimin bayan sun fatattaki ƴan bindigar.
 
Yayin gudanar da bincike, Baba ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka aikata laifin, inda ya bayyana cewa Naira 6,000 aka ba shi a matsayin rabonsa. Ya kuma bayyana sunayen wasu daga cikin abokan aikinsa.

 

Ammaassco

Comment As:

Comment (0)