SHUGABA TINUBU YA AMINCE DA MURABUS DIN GEOFFREY NNAJI A MATSAYIN MINISTA

SHUGABA TINUBU YA AMINCE DA MURABUS DIN GEOFFREY NNAJI A MATSAYIN MINISTA

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din Geoffrey Uche Nnaji, Ministan Kirkire-Kirkire, Kimiyya da Fasaha, bayan zarge-zargen da ake masa.

Shugaba Tinubu ya naÉ—a Nnaji a watan Agustan 2023.

Nnaji ya ajiye aikinsa yau cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kasa, inda ya gode masa bisa damar da ya ba shi na yin wa Najeriya hidima.

Nnaji ya ce ya fuskanci hare-haren batanci daga abokan hamayya na siyasa.

Shugaba Tinubu ya gode masa bisa gudunmawarsa, tare da yi masa fatan alheri a gaba.

*PRESIDENT TINUBU ACCEPTS RESIGNATION OF GEOFFREY NNAJI AS MINISTER 

President Bola Ahmed Tinubu has accepted the resignation of Geoffrey Uche Nnaji, the Minister of Innovation, Science, and Technology, following some allegations against him.

President Tinubu appointed Nnaji in August 2023.

He resigned today in a letter thanking the President for allowing him to serve Nigeria.

Nnaji said he has been a target of blackmail by political opponents.

President Tinubu thanked him for his service and wished him well in future endeavours.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)