Tinubu ya nada Joash Ojo Amupitan (SAN), a matsayin sabon shugaban hukumar INEC na kasa
Tinubu ya nada Joash Ojo Amupitan (SAN), a matsayin sabon shugaban hukumar INEC na kasa.
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), domin maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu.
A wata sanarwa da mai ba wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa Majalisar Ƙasa ta amince da wannan naɗi bayan Tinubu ya gabatar da sunan Farfesa Amupitan.
Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Tinubu zai miƙa sunan sabon shugaban hukumar ga Majalisar Dattijai domin tantancewa da amincewa da shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.
Wannan sabon naɗi na zuwa ne a wani lokaci da ake sa ran ci gaba da gyare-gyare da ƙarfafa sahihancin harkokin zaɓe a Najeriya.
Nagarifmradio




