Tsaron kasa

Gwamnatin Tarayya na Shirin daukar Jami'an Tsaron Sa-kai dubu 130,a Yunkurin ta na Yaki da 'Yan Bindiga

Rashin tsaro: Gwamnatin Taraiya za ta ɗauki jami'an tsaron sa-kai dubu 130 don fattatakar ƴanbindiga 

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin tsaro don fattatakar ƴanbindiga ta hanyar ɗaukar jami'an tsaron sa-kai guda dubu 130, wanda ta sanyawa suna ‘Forest Guards Initiative’.

Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, NSA, Nuhu Ribadu ne ya bayyana hakan a Abuja a yau Alhamis a wajen bude taron shugabannin tsaro na Tarayya da na Jihohi, wato 'Federal and States Security Administrators’ Meeting (FSSAM).

An gudanar da taron a Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa, NCTC, da ke ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, NSA.

NSA ya bayyana cewa sama da jami'an tsaron sa-kai 130,000 da aka horar da su da basu makamai za a tura su a cikin dazuka 1,129 a faɗin ƙasar, inda za a fara da wasu jihohi a matsayin gwaji da su ka haɗa da Adamawa, Borno, Neja, Kebbi, Kwara, Sokoto da Yobe.

Ribadu ya ce wannan shiri, wanda Shugaba Bola Tinubu ya amince da shi, na nuna sauyi mai muhimmanci a dabarun cikin gida na tsaron ƙasa, inda ya ce shirin zai maida hankali kan dazuka da suka dade suna zama mafaka ga ƴantadda.

A Yau News

Comment As:

Comment (0)