Jihar Kebbi
Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ćan Bindiga, Abubakar Abba.
- By NAGARIFMNEWS --
- Saturday, 11 Oct, 2025

- 208 views
AĆalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya Éarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar âyan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.
Wani mazaunin yankin mai suna Ćanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa.
âKashe Sule ya tayar da hankulan alâumma, inda manoma suka Éauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,â in ji shi.
Ya Ćara da cewa makiyayan sun sha faÉa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riĆa wucewa da shanunsu ta gonakin nan ba da daÉewa ba.
âA lokacin da wasu manoma suka je gonakinsu domin yin aiki, sai makiyaya suka kai musu hari, daga nan ne aka shiga tashin hankali,â in ji shi.
Wani mazaunin yankin, Abubakar Aliyu, ya roĆi gwamnati da ta kawo Ćarshen wannan rikici na dogon lokaci tsakanin manoma da makiyaya.
âWannan matsala ba sabuwa ba ce, kuma sarakunan gargajiya sun san da ita. Muna fatan a samu adalci ga waÉanda abin ya shafa, kuma gwamnati ta kawo Ćarshen wannan rikici,â in ji shi.
Rundunar âyan sanda a jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba domin jamiâin hulda da jamaâa na rundunar, CSP Nafiu Abubakar, ba a iya samun sa a waya ba lokacin da ake haÉa wannan rahoto.
Nagarifmradio




