Idan shugabanni sun kauce, bai kamata malamai su bisu a kauce ba, In ji Sheikh Ibraheem El-Zakzaky
Idan shugabanni sun kauce, bai kamata malamai su bisu a kauce ba, In ji Sheikh Ibraheem El-Zakzaky
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya yi kira ga malamai da su tsaya kan gaskiya tare da zama fitila ga al’umma, maimakon bin shugabanni idan suka karkace daga tafarkin adalci.
Sheikh Zakzaky ya jaddada cewa shiru kan zalunci ko bin son shugabanni yana kai al’umma ga rugujewa, saboda haka malamai su rika faɗar gaskiya duk da irin raɗaɗin da hakan zai iya haifarwa.
Ya ce: “Idan shugabanni sun kauce, bai kamata malamai su bisu a kauce ba. A matsayinsu na masu haskaka al’umma, wajibi ne su tsaya tsayin daka wajen kare adalci da gaskiya.”
Nagarifmradio




