Malaman Jami’a Za Su Tsunduma Yajin Aiki Ranar Litinin – ASUU

Malaman Jami’a Za Su Tsunduma Yajin Aiki Ranar Litinin – ASUU

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, ta sanar da cewa za ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu daga Litinin, idan har gwamnatin tarayya ba ta biya bukatunsu kafin ƙarshen wa’adin da ta ba ta.

Wa’adin makonni biyu da ASUU ta bai wa gwamnati ya ƙare ne ranar Lahadi, amma har yanzu ba a ji wani mataki daga bangaren gwamnati ba.

Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana a makon da ya gabata cewa gwamnati tana karshe wajen tattaunawa da ƙungiyar domin warware matsalolin albashi, alawus, da yarjejeniyar da aka kulla tun 2009. Ya ce gwamnatin Tinubu ta saki N50 biliyan don biyan Earned Academic Allowances, sannan N150 biliyan na cikin kasafin kuɗin 2025 domin bukatun jami’o’i.

Alausa ya kara da cewa gwamnati za ta biya sauran bashin alawus da kudaden karin girma kafin shekarar 2026, yana rokon ASUU ta nuna haƙuri da ci gaba da tattaunawa.

Sai dai shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya ce gwamnati ta saba da jinkirta batutuwan da suka shafi malaman jami’a. Ya tabbatar da cewa idan babu wani abu mai gamsarwa daga gwamnati kafin Lahadi, za su tafi yajin aiki.

Rahotanni daga wasu jami’o’in tarayya kamar Jami’ar Jos, Ahmadu Bello University (ABU) Zaria, da University of Abuja sun nuna cewa tuni shirye-shiryen shiga yajin aikin suka fara.

ASUU ta ce wannan mataki yana da nufin tilasta gwamnati ta ɗauki matakin da zai kawo daidaito a harkar ilimi, musamman wajen inganta walwalar malamai da gyaran jami’o’i a faɗin ƙasa.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)