Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba da sahihan bayanai game da masu aikata laifuka, tare da tabbatar musu cewa za a kare sirrin duk wanda ya bayar da irin wannan bayani.

A cewar rahoton Arewa Updates, kwamishinan ’yan sandan jihar, Adamu Elleman, ne ya bayyana haka yayin tattaunawa da manema labarai a birnin Minna.
Elleman ya bayyana cewa rundunar tana gudanar da aikinta cikin ƙwarewa, kuma za ta ci gaba da kare sirrin masu taimakawa da bayanai domin tabbatar da nasarar ayyukanta.
Ya ce raguwar laifuka a birnin Minna da kewayenta na da nasaba da bayanan sirri da jama’a ke bayarwa tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da shugabanni.
Haka kuma, ya ja kunnen shugabannin unguwanni da kauyuka da kada su rika ɓoye masu laifi, inda ya gargade su cewa duk wanda aka samu da hannu wajen kare batagarai, za a gurfanar da shi tare da su.
A Yau News